Jam’iyyar PDP ta bayar da sanarwar jan hankalin jama’a bisa rahotan dake zagayawa na kwace takara daga hannun Abba Kabir.
A cewar jam’iyyar hukuncin kotun ya shafi kadai jam’iyya ne ba dan takara ba, don haka sun daga kara zuwa gaba shi kuma Abba gida-gida yana cigaba da kamfen don samun nasarar zabe mai zuwa ranar Asabar.
Sanarwar dai ta fito ne daga bakin shugaban Jam’iyyar na jihar Kano Rabiu Sulaiman Bichi.
Turawa Abokai