Akwai Rashin Adalci a Auren Mace Fiye da Daya Inji Babban Limamin al-Azhar

214

Wani babban Limami na Jami’ar Al Azhar da ke kasar Egypt yace akwai rashin adalci a cikin auren mace fiye da daya.
Limamin mai suna Sheikh Ahmad al-Tayeb, wanda yana daya daga cikin manyan malamai na Sunna a kasar, ya ce yanda ake gudanar da auren mace fiye da daya akwai rashin fahimtar abin da Allah SWT Ya fada a cikin Alkur’ani.

Ya kara da cewa, mata sune rabin al’umma, haka rashin kula dasu wata nakasa ce kamar mutum ne mai kafa daya. Auren mace daya shi ne wajibi amma idan namiji zai iya adalci a tsakani, an yarda ya kara. In yasan ba zai iya ba, to ya haramta ya kara aure.

Babban limamin ya bayyana haka a cikin shirin sa da yake yi duk sati a gidan talabijin da kuma shafin twitter. Yace akwai bukatan duba akan al’amura da suka shafi mata.

Bayan tafka muhawara, jami’ar al-Azhar tace Limamin ba kira yake da a soke auren mace fiye da daya ba. Shiekh Ahmad shi ne babban limana al-Azhar tun shekarar 2010.

Majalisar mata ta kasar Egypt taji dadin kalaman limamin, kuma sun bayyana ra’ayinsu ta bakin shugabar majalisar mai suna Maya Morsi, wadda ta ce addini musulunci da ya ba mata daraja, da yanci da, kare hakokinsu lokacin da basu da shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan