Jirwaye: Ina Rayuwar Almajiri Ta Dosa A Kasar Hausa? (II)

410

Allah ya sanya Aure tsakanin mace da namiji kuma wannan sha’awa da Allah ya samana alamace ta mu hadu da Allah lafia, amma sai wanda ya sani in mutun be sani ba sai ta zamuwa mutun sababin halaka, dole dan adam yana da sha’awa amma Allah yace ayi aure ya hana bawa yin zina saboda kada afada halaka, to yanzu kayi aure kahaifi yara kuma kana gudun daukar nauyinsu, wanda wannan kwata kwata be dace da addini ba dayawa yara suna zuwa makaranta saboda inganta rayiwarsu ta fuska me kyau.

Duk lokacin da gari ya waye zaka ga yara abin sha’awa suna kan hanyar zuwa makarantar Boko bayan sun dawo da rana zakaga sun sake komawa ta Islamiyya sun zauna gaban iyayensu suna karatu cikin kwanciyar hankali da kulawa ta yau da kullum wannan ba karamin abin alfahari bane a rayiwar dan adam.

Wasu kuwa yaran da ake daukarsu da karancin shekaru ana kaisu bara rayiwa sai dai su kalla su tashi da bakin cikin rayiwa basa kallon iyayensu a matsayin wanda suke kaunarsu, tunda sun dasa gaba a cikin zuciyar yaran da suka haifa da kansu, saboda basusan ina suka kwana ba ina suka tashi babu wanda ya sani tsakanin iyayen da Malaman, wannan ba tarbiyar musulunci bace.

Duk Wanda aka haifa wajibi ne iyayen sa su dauki nauyinsa tundaga kan lafia da Komai da Komai na rayiwarsa saboda ba ganin dama bane wajibine sai an dauki nauyinsu har zuwa shekara (18) bayannan mutun yana da yancin kansa. Tambaya anan dan Allah wane dan sama da shekara (18) aka kaishi bara?

Sai dai kaga yara kanana wanda basusan Komai ba sune wanda ake kaiwa Bara dan Allah yanzu anyi adalci kenan.

Da yawa masana da marubuta sun tafi akan yawan Al’umma ne yake kawo zubar da yara ko gudun daukar nauyinsu da sunan bara to. In kuwa mun yarda da cewa hakane muta kai tawa kanmu mana.

Saboda, da Allah ya kama mutun da hakkin yaransa a ranar sa kamako gwanda baka haife shiba. Saboda ni a iya nazarina kabilar Hausawa ce kawai take haifar yaran da bata iya daukar nauyinsu, haka yana faruwa wajan biyewa san zuciya na aure ba tare da kiyaye hakkin auren ba duk wanda yake da mace fiye da daya to zai tara yara.

A nazarina da nayi na yau da kullun da zamantakewar rayiwar dan adam, ko kabilar da nafito babu wanda yake tara mata a Gida sai Malam me karamin karfi wanda shi gani yake kamar hakan addini ne ya sashi to koma dai ya abin yake wannan aikin Malaman addini ne.

lokaci yayi da yawan mutanan kasarmu zai anfanar da kasar, bincike ya nuna Nigeriya itace kasa ta (7). A yawan mutane wanda yanzu haka yawanmu ya Kai 192,259,546 yanzu saboda Allah wanne tana di mukayiwa kanmu.

Kai kananan yara Bara bashi ne tana di me kyau ba wannan rusa rayiwarsu ne a matsayinsu na yara matasan gobe duk da muna sane da cewa akwai kasa daya a duniya wanda itace kasar da tafi kowacce kasa yawan Al’umma da sukaga abin zai wuce tunaninsu kuma tana dinsu yayi kadan, daga karshe me sukayi dole ta sakasu sukayi tsarin iyali, wanda haka be sabawa tsarin kasarsu ba. indai mum san yaranmu da muke haifa baza mu iya daukar nauyinsu; to muma muyiwa kanmu tunani me kyau mana.

Addinin musulinci, addini ne na masalaha da zaman lafia ba, addini bane na gama garin mutane addini ne wanda yazo da tsari da sauki, amma sai mu dinga bata sunan addininmu da kanmu, abinda yasa na fadi haka aikinmu ne ya nuna haka.

Duk lokacin da kake gida a zaune zakaji Al’majiri yazo yana bara kana tafia a kan hanya zakaga yana bara to indai karatu yazo me ya hadashi da bara indai ba gudun daukar nauyinsu ba, daga bangaran iyaye me yasa baku turosu da kayan abinci da zasu ci ba duk da na sani kunsani duk wanda zaiyi karatu yana bukatar kulawa ta musanman, yanzu Al’majirai da suke yawo cikin rashin tsafta da kaya Marasa kyan gani, addini ne ya tanadi haka.

Ba addini bane ya tanadi haka san zuciya ne nakanmu.

Shu’aibu Lawan

Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560 (Text Only).

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan