Ni ne ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano- Abba

161
Abba Kabir Yusuf

Duk da hukuncin da kotu ta yanke ranar Litinin a jihar Kano wanda ya soke zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP ta ce ta yi, Abba Kabir Yusuf ya dage cewa shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar.

Wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a jihar Kano ce ta soke zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP a jihar Kano ta ce ta gudanar.
Kotun ta yanke hukuncin cewa Abba Kabir Yusuf ba zai zama dan takara halatacce ba har sai an sake gudanar wani sabon zaben fitar da gwani.

To amma lokacin da jaridar The PUNCH ta tuntube shi, Abba ya ce shi ba ya daga cikin wadanda ake kara a karar da Ibrahim Al’amin Little ya shigar, ya ce jam’iyyar PDP ake kara, ya kara da cewa jam’iyyar ta dauki matakin da ya dace.

Abba Kabir Yusuf ya ce zai ci gaba da yakin neman zabe har zuwa ranar Alhamis da daddare, ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu su kuma ci gaba da yaƙin neman zabe don tabbatar da nasararsa a zaben 9 ga watan Maris.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan