Wasiyyoyi 5 Daga Manzon Allah (S.A.W)

364

Manzon Allah (s.a.w) yace: “Waye zai karbi wadannan Kalmomi guda 5 daga gareni, yayi Amfani da su, ko ya Sanar da wanda zai yi Amfani da su”

Sai Abu Huraira (R.A) yace Ni Zan karba ya Ma’aikin Allah.

Sai Manzon Allah (s.a.w) ya rike Hannu na yace min:-

1. Ka guji Aikata Sabo, Zaka Zamo wanda yafi kowa wauta a cikin Mutane.

2. Ka yarda da Abinda Allah Ya baka, Zaka fi Kowa Arziki Cikin Mutane.

3. Ka kyautata wa Makobcin ka, Zaka Zamo (cikakken) Mumini.

4. Ka So Wa Mutane Abinda Kake So Wa Kanka, Zaka Kasance (cikakken) Musulmi.

5. Kada ka Yawaita Dariya, Domin Yawan Dariya na Kashe Zuciya.

“Manzon Allah (S.A.W) Yace Ka Rike su Ko ka Sanar da Wanda Zaiyi Amfani Dasu”.

Idan ka Tura Wa ‘Yan Uwa Musulmai Baka San Wa Zaiyi Amfani Dasu Ba, Kaga Ka Samu Ladan Mutane Masu Tarin Yawa.

Ubangiji Allah ya bamu ikon aikatawa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan