Buhari ne zai zaɓi Shugaban Majalisar Dattijai mai zuwa- Omo Agege

182
Sanata Ovie Omo Agege

Sanata mai wakiltar Delta ta Tsakiya, Ovie Omo Agege ya ce Shugaba Muhammadu Buhari zai yi uwa ya yi makarbiya wajen samar da shugabanci Majalisar Datta na gaba.

Da yake jawabi ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN a Warri, Mista Omo Agege ya ce Shugaban Kasar da jam’iyyar APC mai mulki za su guje wa maimaita kuskuren da ya faru a 2015 inda Dakta Abubakar Bukola Saraki ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

“Duk wanda zai zama Shugaban Majalisar Dattija, a Majalisar Dattijai ta 9, dole ya zama mai biyayya ga Shugaban Kasa, mai biyayya ga jam’iyya da Kundin Tsarin Mulki.

“Shugaban Kasa ne zai ce ga Shugaban Majalisar Dattijai.
“Shugaban Kasa zai nuna mana wanda yake so ya yi aiki tare da shi ta hanyar jam’iyya”, in ji Sanata Omo Agege.

Jam’iyyar APC mai mulki ta shirya samar da Shugaban Majalisar Dattijai na gaba bayan lashe mafi rinjayen kujeru a Majalisar Dattijan a zaben 23 ga watan Fabrairu.

Da aka tambaye shi ko APC ta mayar da Shugabancin Majalisar Dattijai zuwa wani sashin siyasa, sai dan Majalisar ya ce: “Ban sani ba”.
“Amma abinda zan iya fada muku shi ne za mu samu Majalisar Dattijai wadda za ta yi aiki da Shugaban Kasa.

“Lokacin da za a kyale ‘yan tawaye masu hawa doron bayan Shugaban Kasa da doron bayan jam’iyya su je can su siyar da bukatar jam’iyyar, ina jin wannan lokacin ya wuce.

“Ina da kyakkyawan fatan cewa a wannan karon Shugaban Kasa zai shigo ciki ya fadi ba wai kawai sashin da zai samar da Shugaban Majalisar Dattijai da shugabancin ba, amma wane ne ma ya kamata.

“Ba ma so mu kara kafa wani shugaban hamayya a Majalisar Dattijai kamar yadda muka gani a Majalisar Dokoki ta Kasa ta 8.
“Akwai da yawa daga cikin mu wadanda za su dawo Majalisar Dattijai ta gaba wadanda sun cancanci wannan mukamin.

“Muna da yawa, amma duk hukuncin da Shugaban Kasa ya yanke, gaba daya za mu karba kuma mu yi biyayya”, a kalaman Sanatan.

Sanata Omo Agege ya ce APC nada damar samun nasara a zaben gwamnoni na ranar 9 ga watan Maris a jihar Delta, yana mai karawa da cewa: “Al’ummar jihar Delta sun lashi takobin ba za su kara zama a cikin hamayya ba”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan