Hanyoyi 5 Da Zaka sa Tsohon Masoyi Nadamar Rabuwa a Soyayya

4570

Idan wani dalili yasa aka samu matsala a tsakanin masoya, kuma hakan yayi sanadin rabuwa, akwai hanyoyi da masoya zasu iya bi wajen gyara alakarsu.

Wani sa’in, masoya kan daura laifin rabuwa kacokam akan daya daga cikin su. Hakan zai sa daya daga cikin masoya ya dinga ganin cewa an zalunce shi a cikin alakar kuma ya zama wajibi ya dakatar da alakar.

Don haka, akwai hanyoyin da mutum zai iya bi domin sa tsohon masoyi yin nadamar rabuwa.

Tabbatar da cewa masoyi ya gane barin alakar a wannan lokaci babban kuskure ne. Hakan kuwa yana bukatar masu daidaitaccen lokaci ba tare da roke-roke ba.

Sanin irin matakin da zai biyo, Ya kamata mutum ya zama a cikin shiri domin kuwa idan bukata ta biya, to masoyi zai dawo. In kuma hakan bai samu ba, zai iya zama matsala da zai kara nisanta alakarsu.

Saka masoyi tsoron barin alakar.
Hakan zai yiwu ne idan masoyi yasan daraja da kimar mutum kuma hakan zai sa yaji tsoron barin alakar domin kuwa zai yi babban asara a rayuwa.

Tunasar da masoyi irin lokuta mafi muhimmanci na alakar da aka yi. Hakan zai sa yaji baya son alakar ta kare.
Amfani da irin abubuwan alkairi da kyautatawa domin karfafa alakar.

Duk wani abun kirki da ya gudana, yi kokarin maimaitawa ko kuma yi amfani da salon dabara don tunawa masoyi. Hakan zai sa masoyi ya dawo da alakar soyayya ko da kuwa ya fasa a baya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan