Ina aka Kwana kan Tsige Sarkin Musulmi?

205

Kungiyar Muslim Right Concern (MURIC) ta bayyana damuwarta bisa zargin da ta ke na shirin sauke mai martaba sarkin Musulmin Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.

Kungiyar ta jadada cewa ya zama wajibi a baiwa mai martaba sarkin musulmi kariya daga tsigewa.

Directan kungiyar, farfesa Ishaq Akintola a wani sanarwa da ya fitar, ya ce suna bukatar tabbaci daga jam’iyyar APC domin matsayin sarkin musulmi ba mukami bane da wani gwamna ko shugaban kasa zai wayi gari ya ce zai tunbuke shi ba. Shugabanci ne na musulmin Najeriya baki daya, don haka ya kamata a yi wani tsari da zai karfafa tsarin masarautar.

A ranar litinin dubun dubatan matasa suka gudanar da zanga-zanga a cikin gari zuwa fada, don nuna bacin ransu akan lamarin.

Murtala Abdurrahman daya daga cikin shugabannin matasan da suka yi zanga zangar ya tattauna da manema labarai inda yace, sun fito ne don sanar da sarkin musulmi manufar jam’iyyar APC na tsige shi idan sun samu mulki a zaben da za’a yi na gwamna kuma ba zamu bari su bata mana tsarin al’adar mu ba.

Shugaban jam’iyyar APC ta jihar Sokoto Isa Acida, ya zanta da manema labarai a sakatariyar kungiya inda yace aikin jam’iyyar adawa ta PDP ne akan zaben da za’a yi na gwamna.

Ya kara da cewa, sunyi hakan ne don su tada hatsaniya a jihar ta Sokoto kuma jam’iyyar APC tana zargin shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Milgoma da yada wannan jita-jita.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan