Wani Magidanci Ya Yiwa Matarsa Ƙaryar Kurmantaka Tsawon Shekaru 62

177

Wani mutum mai suna mista Dowry Dawson mazaunin garin waterbury a jihar Las anjalas a ƙasar Amurka, ya gurfana a gaban kuliya sakamakon yi wa matarsa ƙaryar kurmantaka har tsawon shekaru 62.

Mutumin a cewar lauyansa ya yanke yin hakan ne domin ganin aurensu ya yi ƙarko. Saboda ya Lura matar ta sa na da matsalar surutu, shi kuma mutum ne mara san haka.

Da ta ke bayar da bahasi a gaban kotu Mis Dawson, ta ce sai da na tilastawa kaina koyon yaren kurame, inda ya ɗaukeni shekaru 2 inayi.

Ta ƙara da cewa wani abin haushin shi ne bayan na ƙware a wannan yaren sai ya fara ƙaryar cewa baya gani sosai, inji ta.

A lokacin da dubunsa za ta cika, Matar Dawry Dawson ta ganshi yana rera waƙa ne a wajan wata walima, inda abin yayi matukar ba ta mamaki tare kuma da hasalata.

Tun da farko mutumin mai shekaru 84 da matarsa ƴar shekara 80 na da ƴaƴa 6 da jikoki 13, dukkan waɗannan iyalan tsawon lokuttan da suka yi da shi a matsayin kurma su ke ganin sa.

Yanzu haka dai matar ‘yar shekaru 80 na bukatar raba auren su, saboda abin da ta kira yaudara, da rainin hankalinta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan