Zan yi aiki tuƙuru wannan karon- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zai yi aiki tukuru wannan karon don kar ya kunyata ‘yan Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da Kungiyar Tuntuba ta Arewa, ACF ta kai masa ziyara a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

ACF din ta kai masa ziyara ne don ta taya shi murnar sake zaben sa da aka yi.

Buhari ya fada wa Kungiyar wadda Shugaban Kwamitin Amintattunta, Alhaji Adamu Fika ya jagoranta cewa: “Wannan ita ce damata ta karshe, zan yi kokarin yin aiki tukuru. Ina mai tabbatar muku ba zan ba ku kunya ba”.

Da yake jawabi tunda farko, Alhaji Fika ya ce Kungiyar ta gamsu da kokarin Buhari a wa’adin mulkinsa na farko musamman wajen aiwatar da wasu muhimman aikace-aikace kamar aikin Tashar Jirgin Ruwa ta Kan Tudu ta Baro dake Arewa.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan