Kwan gaba kwan baya: Kotu ta ce Abba Kabir Yusuf zai yi wa PDP takarar gwamna a Kano

54
Abba Kabir Yusuf

Labarin da BBC Hausa ta wallafa na cewa wata Kotun Daukaka Kara a Kaduna ce ta yi watsi da hukuncin da wata Kotun Tarayya a Kano ta zartar wacce ta rushe zaben da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Kano wanda ya bai wa Abba Kabir Yusuf damar zama dan takarar gwamna a jam’iyyar.

BBC ta ce Alkalin Kotun Daukaka Karar a Kaduna Daniel O. Kalio ya jingine hukuncin da kotun Tarayya ta Kano ta zartar tare da yin umurni ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC kada ta yi aiki da umurnin kotun ta Kano.

A cewar BBC Hausa, Kotun yanzu ta ba bangarorin biyu kwana biyar su gabatar da bayanai domin yin nazari kafin ta sake yin zama domin sauraren daukaka karar da bangaren Kwankwansiyya ya shigar.

A ranar Litinin, 4 ga watan Maris ne Babbar Kotun Tarayya ta Kano ta rushe zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP ta yi, wanda ya ba Abba Kabir Yusuf damar zama dan takarar gwamna.

Dan takarar gwamna a jam’iyyar ta PDP, Ali Amin-little ne ya shigar da karar inda yake kalubalantar zaben da har Abba Kabir Yusuf ya zama dan takara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan