Ra’ayi: Zaɓen Gwamnan Kano: Gaba Kura baya Siyaki

72
Taswirar Jihar Kano

Daga Ali Abubakar Sadiq
08039702951
aleesadeeq1@yahoo.com

Tun lokacin da aka fara zaben gwamna a Kano a shekarar 1979 inda a ka kara tsakanin Abubakar Rimi da Aminu Bashir Wali, zuwa shekarar 1983 da aka gwabza tsakanin Rimin da Sabo Bakin Zuwo, har lokacin zaben 1990 tsakanin Magaji Abdullahi da Kabiru Gaya, an sami canji daga masu ra’ayin gaba-dai-gaba-dai da yan jari hujja.

A jamhuriyya ta hudu wadda muke ciki yanzu kuwa, wannan yaki ya ci gaba a lokacin da aka kara tsakanin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Magaji Abdullahi a 1999, sannan aka sake karawa da Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau a 2003, aka sake wata karawar tsakanin Shekarau da kuma Ahmed Garba Bichi a 2007, sannan aka sake karawa tsakanin Kwankwaso da Malam Salihu Sagir Takai a 2011, har ya zuwa wannan lokaci na zaben 2019 inda za a kara tsakanin Dakta Abdullahi Umar Ganduje (gwamna mai ci) da Abba Kabir Yusuf.

A duk wadancan zabuka na baya Kanawa basu taba fuskantar tsaka mai wuya ba, abinda Bahaushe ke cewa “Gaba kura baya Siyaki” kamar irin wannan zabe.

Abin tambaya a nan shi ne shin Kanawa sun cancanci fuskantar yanayin da su ke fuskanta a wannan zabe? Kafin na bada amsa na warware zaton da wasu ke yi na cewa to ai akwai dama ta uku, wato, Malam Salihu Sagir Takai. Takai ba don ya ci yake yi ba. Domin duk wanda ke nazarin yadda siyasa ke gudana a kasar nan, zai lura da cewa jam’iyya ta uku ba ta taba cin zabe. Jamiyya mai mulki ko mai adawa kadai ke iya cin zabe saboda dalilai da dama. Jam’yyar adawa na iya kwatar mulki a hannun jam’iyya mai mulki amma ba dai wata ta uku ba. Tunanin mutane ya ginu da yin cincirindo a wadannan jam’iyyu guda biyu don haka su ke da kuri’u da zasu iya cin zabe kawai. Hanyar da jam’iyya ta uku za ta iya tasiri kawai shi ne idan ta zabi jam’iyya mai mulki ko adawa ta goya musu baya, don haka da wahala Taka ya yi tasiri.

Mene ne dalilin da ya sa muka samu kanmu cikin tsaka mai wuya a Kano? Wannan ya samo asali ne daga irin ‘rikon sakainar kashi’ da al’umma gaba daya suka yi wa harkar shugabanci. Shugabanci shi ne abu mafi mahimmanci sama da komai a al’ummar da ta san kanta. Shi yasa a kasashe da su ka ci gaba masu fada-a-ji sukan dunkule tun kafin zabe su samar wa mutanensu ‘yan takara jajirtattu wadanda kowaye ya ci zai saka muradu da buatar al’ummar nan ne a gaba sama da son kansa.

Dalilin da yasa Kano ta ci kirarin “Tumbin Giwa” shi ne a baya shugabanninta jajirtattu ne kuma sun dauki shugabanci da muhimmanci yadda ba kowane kare da doki ke jan akalar mutane ba. A baya lokacin mulkin mallaka, Kano ta yi dacen shugaba jajirtacce, wato Abdullahi Bayero, wanda ya hada kan masu fada a ji na Kano wuri guda su ke yi mata tunani da aiwatar da abubuwa na ci gabanta.

Tun a shekarar 1949 Hukumar Native Authority (N.A) ta Kano ta shata jadawalin ci gaba na jihar Kano mai gajeren zango na shekaru biyar wanda daga baya a ka fadada shi ya zama na shekaru 10. A karkashin wannan tsari a ka habbaka noma, musamman na gyada tare da samar da Hukumar Kula da Kasuwanci (Marketing Board) wadda dilallanta na farko Kwarori ne wadanda tun shekarun 1930 su ka fara kasuwanci a Kano. Daga baya Sarki Abdullahi ya sa ‘yan kasa suka fara karbar lasisin dillanci abinda ya haifar da hamshakan masu kudi a birnin Kano inda a ka sami Alhassan Dantata, wanda ya fi kowa kudi a yammacin Afirka, kuma Kano ke samar da kusan kaso 50 na kudaden da ake gudanar da Nigeria a wancan lokaci. Sarki ya sa aka dinga tilasta talakawa shiga Makarantun Boko duk da cewa ana kyamar Ilimin Boko a wancan lokaci, ta hanyar saka duk ‘ya’yan masu sarauta a Makarantar Boko yadda talaka zai yadda ya mika wuya.

A wancan lokaci Kano ke samar da kusan rabin kudin kasafin Najeriya. Bayan Yakin Duniya, Kano na da madaba’u na buga takardu guda shida na ‘yan kasuwa banda guda daya ta N.A.

A lokacin, a fadin Arewa kaf babu madaba’a shida. Amma bayan rasuwarsa da zuwan Sarki Sunusi sai abubuwa suka fara ja baya saboda maimakon a maida hankali kan noma da ilimi sai a ka koma kan harkar addini, rikicin shugabanci da sharholiya da kudaden gwamnati.

A yanzu Kano na da dimbin mutane masu alfarma ta kowacce fuska, wasu sun shahara a duniya, misali dauki Sarkinmu na yanzu, gogaggen masanin Tattalin Arzikin ne, mai Ilimin Boko dana addini kuma hamshakin attajiri. Aliko Dangote ya gaji kakansa har ya zarce shi a matsayin mafi kudi ba a Afirka ta Yamma kawai ba har ma a duniya. Muna da ‘yan siyasa irin su Bashir Tofa da ya yi takarar shugaban kasa da Abiola, ga malamai irin su Malam Ibrahim Khalil banda malamai farfesoshi masu tarin yawa daga kowanne sashe na ilimi. Amma duk sun zama taron yuyuyu domin sun kasa sauke nauyin da Allah Ya dora musu na tsayawa su jajirce wajen ganin cewa lallai sai shugabannin masu inganci ne za su shugabance mu.

Mun fi kowa yawan jama’a da tarin arziki amma mu ke da mafi yawan almajirai da marasa aikin yi, shin dora wa Allah laifin halin da muke ciki bayan ya ba mu duk abinda ake bukata domin samun ci gaba?

Marigayi Malam Aminu Kano ya yi iya kokarinsa wajen wayar da kan talaka ya gane muhimmanci kuri’arsa tare da fitar da jadawalin ceton al’umma na PRP kuma kowa ya ga yadda wannan jadawali karkashin mulkin Rimi ya farfado da harkokin ilimi, noma, ayyukan raya kasa da samar da wutar lantarki da sauran abubuwa wadanda Audu Bako ya faro.

Lokacin da Kwankwaso ya dawo mulki a karo na biyu tare da dabbaka jadawalin PRP na farfado da ci gaban ilimi da ayyukan raya kasa, ya gaza wajen saka harkar noma. Illar Kwankwaso ita ce ya kasa gane irin baiwar da Allah ya yi masa, domin a fadin Najeriya idan ka cire Shugaba Muhammadu Buhari babu wani dan siyasa da zai daga hannunsa mutane su bi shi ba don komai ba sai don kauna saboda nuna ya na kishin talaka kamar sa. Matsalar ita ce sabanin Buhari wanda domin Allah yake haka, shi Kwankwaso yana yii ne domin siyasarsa kawai. Yawancin abubuwa yana yin su ne domin a gani ne kawai. Amma da tunaninsa irin na su Buhari da Aminu Kano ne da WalLahi babu shugaba kamar sa. Ya kasa koyi da Ahmed Bola Tinubu yadda cikin wadannan shekaru na jamhuriyya ta hudu ya kasance shugaban Yarbawa.

Kano nada matukar bukatar sabon Aminu Kano, kuma Kwankwaso kadai ya sami damar ya yi watsi da ita.
Ganduje ya dare kujerar mulki tare da wasu damammaki da Allah Ya ba shi, kasancewar ya yi shekaru takwas a matsayin Mataimakin Gwamna sannan ga shi shekaru sun hau kansa sosai, amma maimakon ya gode wa Allah ya tsaya tukuru wajen ganin ya bar tarihi na gina jihar da al’ummar sai yake ganin idan ya rike hannun Buhari kawai kuma ya yi mana ‘yan gadoji na sama shike nan za a sake zabensa. Ya manta cewa ya shekara ashirin yana hakilon Allah ya bashi kujerar kuma ya ba shi, amma sai ga shi maimakon yasa a yi gaba sai baya a ake yi.
Domin zuwansa ya dawo mana da siyasar banga wadda a baya kasacewar samuwar gidajen rediyo da sojojin baka an daina banga. Ya yi watsi da harkar ilimi duk da cewa gwamnatin da ta gabata ta samar da ajujuwa daruruwa da kuma makarantu da dama. Kwanaki na ga wani ajin ‘yan firamare a karamar hukumar Nasarawa da dalibai sama da 500, yadda malami ba zai iya zarya a aji ba sai dai ya dinga tsallake dalibai banda wadanda su ka toshe tagogin ajin saboda cincirindo.

Kudaden da wannan gwamnati ke kashewa wajen tallace-tallace a kafafen watsa labarai na kudancin kasar nan sun isa su farfado da Gidan Talabijin na Abubakar Rimi (CTV a da) da Radio Kano. An wayi gari a gwamnatinsa sai da Gidan Rediyon Kano ya dain watsa shirye-shirye na wani zango saboda karancin kudi, abinda bai taba faruwa a baya ba.

Dalibai da aka tura kasashen waje sun shiga halin kaka-ni-kayi saboda rashin biya musu kudaden makaranta duk da cewa wasu a shekarun karatunsu na karshe suke. Kwankwaso ya kwashe kudaden ‘yan fansho ya gina biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo amma an bar su suna lalacewa yadda har kayayyakin gidajen an fara babballe su. Shekara hudu a bar kadarar mutane ta biliyoyi na lalacewa haka? Shin da kudin Ganduje ne zai yarda ya barsu haka? Filayen badala, masallacin idi, kasuwanni har da na makabarta wannan gwamnati na ta rarraba su ga mutane manya a jihar nan kuma sun yi tsit.

Ana daukar kudaden gwamnati ana ba wa malamai domin a toshe musu baki, kuma hakan ya bayyana karara lokacin da malaman Izala, maimakon su yi shiru kan fitar da bidiyon badakalar da gwamna ke karbar kudade sai ga shi sun yi masa mubaya’a a gidan gwamnati har da jawo hadisai don kare shi. Malami daya tilo da ya ce a yi adalci wajen bincike sai ga shi an yi masa ca a gidajen rediyo da kafofin sadarwa daga karshe ma an rufe ofishinsa.

Abin farin ciki shine, yadda zaben 2019 ya nuna shi ne masu jefa kuri’a a duk fadin kasar nan sun fara wayewa domin mun ga yadda mutanen Kwara suka kori Bukola Saraki daga kan kujerarsa ta Shugaban Majalisar Dattawa, bayan gwamnati ta yi iya kokarinta na ta tsige shi abin ya gagagara. A salin alin talakawa suka kore shi. Haka aka yi wa Ajimobi da Dankwambo da Akpabio.

A daya bangaren kuma, duk da cewa Gwmantin Tarayya da gwamnatocin jihohin su Dino Melaye da Yakubu Dogara ba sa tare da su, sai ga shi talakawansu sun maida su kan kujerunsu na ‘yan majalisa. Kada mu manta cewa wannan sabon salo a Najeriya, tsoho ne a jihar Kano domin tun shekarar 1983 talakawa suka kori gwamna Rimi yana kan kujerar gwamna su ka dora Sabo Bakin Zuwo. Munga yadda duk da farin jinin dan takara da jam’iyya, wato Magaji Abdullahi na SDP, aka wayi gari Kabiru Gaya na NRC ya kada shi. Mun kuma tuna yadda Shekarau ya kada Kwankwaso da yake kan kujerar. Haka dai Kwankwason a lokacin dawo-dawo ya kwace mulki daga hannun su Shekarau a 2011.

Duk da cewa zaben gwamnan na wannan Asabar din tamkar Gaba Kura Baya Sayaki ne, wajibi mutane su auna su zabi, ko dai wanda cin hancinsa da rashawa ya bayyana karara, da gazawa wajen tallafa wa ilimi da talakawa, da kuntata haraji ko su zabi wanda zai tallafi ilimi, da matasa amma za a iya juya shi. Ko menene dai, ya rage talaka ya yi wa kansa zabi, kuma alhamdu lilLahi, talakawa sun waye da gane cewa su ke da zabi, kuma Bahaushe na cewa “Da bakikkirin gara baki-baki”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan