Ya ga samu ya ga rashi: Kotu ta soke zaɓen da aka yi wa wani sabon ɗan Majalisar Dokoki a Adamawa

121
Gudumar Alƙali

A jiya ne wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Yola ta soke zaben da aka yi wa Abdurrauf Moddibo dan Majalisar Dokoki a karkashin tutar jam’iyyar APC wanda zai wakilci Mazabar Tarayya ta Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei.

Dan majalisa mai ci na yankin, Lawal Garba ne ya maka sabon dan Majalisar Dokokin ta aka zaba din a kotu bisa zargin cewa zaben fitar da gwani da ya ba dan Majalisar nasarar zama dan takarar jam’iyyar APC bai kammala ba.

Kotun ta yanke hukunci cewa jam’iyyar APC ba ta gabatar da dan takara a Mazabar Tarayya ta Yola ta Arewa, Yota ta Kudu da Grei ba.

Da yake gabatar da hukuncin, Mai Shari’a Abdulaziz Anka ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC da ta janye Takardar Shaidar Cin Zabe da ta ba Moddibo ta kuma bada irin wannan Takardar Shaida ga dan takarar jam’iyyar PDP da ya zo na biyu a zaben, Jafar Ribadu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan