Home / Siyasa / Zaɓen gwamnoni: INEC ta fara raba kayan aikin zaɓe a Kano
Akwatin zaɓe

Zaɓen gwamnoni: INEC ta fara raba kayan aikin zaɓe a Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC a jihar Kano ta fara rarraba kayan aikin zabe masu bukatar kulawa a jihar.

Mataimakin Daraktan Sashin Hudda da Jama’a na INEC a Kano, Alhaji Garba Lawal ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN a Kano ranar Alhamis.

A ta bakinsa, tun ranar Laraba ma’aikatan INEC suka fara shirya kayan aikin zaben masu bukatar kulawa musamman takardun kada kuri’a ga kowace karamar hukuma.
Ya ce raba kayan aikin da aka fara ranar Laraba za a kammala shi ne ranar Juma’a.

“Dama tuni kayan aikin zaben masu bukatar kulawa suna ofisoshinmu na kananan hukumomi tun bayan da aka kammala zaben Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisun Dokoki.

“Saboda haka, muna kokarin raba kayan aikin zaben masu bukatar kulawa ne kadai daga nan zuwa Juma’a don saukaka wa ma’aikatanmu da kuma matasa masu yi wa kasa hidima yadda za su isa wuraren da za su yi aikin a kan lokaci ranar zabe”, in ji shi.

Game da batun dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Kakakin na INEC ya ce har yanzu Ofishin INEC na Kano bai karbi wani umarni ba daga Shelkwatar Hukumar Zabe dake Abuja.

Idan dai za a iya tunawa ranar Litinin, 4 ga watan Maris ne wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Kano ta soke zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP ta ce ta gudanar wanda ya ba Abba Kabir Yusuf nasara.

Kotun ta umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da wani sabon zaben fitar da gwani don ba ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar damar yin takara.

About Hassan Hamza

Check Also

Shugabannin Addini Da Na Siyasa Na Ƙoƙarin Kifar Da Gwamnatina— Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta ce wasu ‘yan Najeriya marasa kishin ƙasa na ƙoƙarin haɗa kai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *