Bincike: Shin Da Gaske Likitoci Sun Gano Maganin Cutar HIV?

381

Liktoci sunyi wa wani mai fama da cutar kanjamau a kasar ingila aikin kuma sakamakon haka, an kasa gano kwayoyin cutar a jikin majiyyacin.

Hakan ya karfafa wa likitocin gwiwa, ganin cewa zasu iya samar da hanyar da za’a magance cutar kanjamau a duniya.
Gidan Radion BBC hausa sun rawaito cewa an kasa gano cutar AIDS a jikin wani mutum mai dauke da cutar bayan da aka yi masa dashen sabbin kwayoyin hallita, kuma wannan ne karo na biyu da likitoci suka yi irin wannan gwaji.

Zuwa yanzu, majiyyacin ya kwashe tsawo watanni 18 ba tare da shan maganin cutar ba kuma babu alamar ciwon a tare da shi. Wasu masana ne daga jami’o’in landan da Imperial da Oxford da Cambridge suka hada kai wajen gudanar da wannan aiki, kuma suna ganin aiki zai zama babban mataki wajen magance cutar.

Kwayoyin cutar Kanjamau na iya rayuwa ne a jikin mutum mai dauke da kwayoyin hallita na CCR5, kuma akwai tsirarun mutanen da basu da wannan kwayoyin hallita a duniya. Don haka masana suka kirkiri yin dashe bargo na mutum, da baya dauke da wannan kwayoyin hallita ga mara lafiya.

Bayan anyi wa mara lafiyar dake kasar landan dashe, sai aka ga jikin sa ya daina daukar kwayar cutar HIV, duk da cewa an samu ragowar kwayoyin cutar amma basu yi tasiri a jikin majiyyacin ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan