Rundunar YanSanda na jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu bata gari guda 24 a jihar.
Kwamishinan YanSandan jihar, mallam Ahmad Abdurrahman ne ya bayyana haka, a jiya Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai.
Malam, Ahmad yace, rundunar ta samu nasarar kama mutane bayan da ta gudanar da aiki na musamman a kokarin ta na kawar da barayi daga jihar.
Ya kara da cewa, a cikin wanda aka kama, akwai mutum biyu da ake zargin da yin garkuwa da mutane.
Kwamishinan yace sauran mutanen an kama su ne da laifin hadin baki ayi barna, fashi da makami, da Sayan kayan sata, da kwacen mota, da haurawa gidan jama’a, da sata, da rike makamai ba bisa ka’ida ba, dabanci da sauransu.
Daga nan, sai ya bayyana abubuwan da aka kama mutanen dauke da su, wanda Suka hadar da; pistol guda Uku, da jigidan harsashi guda 15, da bingigar Dane guda daya, da bindigogin gargajiya guda hudu.
Bayan haka, rundunar ta karbo motocin Toyota guda tara, da laptops guda goma, da wayar Galaxy tab, da wayar Samsung duo handset, da sabuwar turmin Atamfa, da Agogo, da takobi, da dogon lauje, da ganga da, kuma jacket na sojoji, da wandon yan sanda, da bakin yadi guda biyu da belt na yansanda guda biyu, decoder guda biyu sai kuma Adda, daga hannun su.
Mallam Ahmad yace, mutanen sun yi bayanai masu muhimmanci kuma za’a mika su kotu da zarar an gama bincike.
Daga nan yayi kira ga yan siyasa a jihar da su guji yin maganganun batanci a lokacin zabe. Sannan su daina amfani da matasa don aikin dabanci saboda a samu a yi zabe lafiya.
A karshe, yayi kira ga al’umma da su kasance masu taimakwa rundunar ta hanyar kawo rahotannin aikin bata gari sai kuma ya jadada kokarinsu na yaki da crime.