Ko kun san dalilin da yasa INEC ta ɗaga zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Adamawa?

138
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC Farfesa Mahmud Yakubu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta daga zaben Majalisar Dokoki ta Jihar Adamawa a mazabar Nasarawa/ Binyeri.

Kwamishinan INEC a jihar Adamawa, Mista Kashim Gaidam ya tabbatar da haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ranar Alhamis a Yola.
Mista Gaidam ya ce dage zaben ya zama wajibi sakamakon rasuwar dan Majalisar Dokokin Jihar wanda shi ne dan takarar jam’iyyar APC a zaben.

NAN ya bada rahoton cewa har lokacin da ya rasu ranar Laraba, Mista Adamu Kwanate shi ne dan Majalisar dake wakiltar mazabar.
Marigayi Kwanate ya fadi ne lokacin da yake yakin neman sake zaben sa, bayan nan kuma ya rasu a wani asibiti a Yola.

Mista Gaidam ya ce daga zaben zai ba jamiyyar APC da al’ummar yankin damar maye gurbin dan Majalisar.
“Mun samu wasika daga jam’iyyar da kuma Majalisar Dokoki game da rasuwar dan takarar, kuma mun ba su amsa, inda muka ba su mako guda don su samo wanda zai maye gurbin sa.

“Za mu isar da wanda suka maye gurbin sa da shi zuwa shelkwata don su saka wata sabuwar ranar zabe”, a cewar Mista Gaidam.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan