Zazzafan Hukuncin Wanda Aka Kama Yana Sayan Ƙuri’u A Lokacin Zaɓe

229

Shugaban Hukumar EFCC shiyyar Kaduna, malam Mailafiya Yakubu yace sayan Kuri’u a lokacin zabe laifi ne da yake dauke da hukuncin shekara 12 a gidan yari ko kuma tarar naira 500,000.

Dan haka, shugaban ya ja hankulan yan siyasa da su guji sayen zabe a zabukan gwamnoni da na yan majalisu da za’a yi.
A ziyarar da ya kai ofishin shugaban kungiyar yan jarida reshen jihar kaduna ( Nigerian Union of Journalist), a jiya, malam Yakubu yace yan jarida zasu taimaka wajen yaki da rashawa kuma hukumar su a shirye ta ke wajen hada kai da yan jarida don yakin cin hanci da rashawa, da yakar sayan kuri’u a lokacin zabe.

Shugaban kungiyar NUJ na jihar Kaduna, mallam Adamu Yusuf ya yabawa shugaban hukumar ta EFCC bisa ziyarar da ya kai musu kuma ya tabbatar masa da zasu basu hadin kai domin cigaban kasa.

Malam Yakuba ya kara da cewa, shi abokin kowa ne, don haka yayi kira ga al’umma da su sami sayan kuri’u babban laifi ne, don haka ya kamata su sauke nauyin da ya rataya a kansu ta hanyar tona asirin masu yi. Kuma hukumar su tana aiki ta jam’an tsaro don bankado asirin masu saye da masu sayar da kuri’u.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan