A bayyana sakamakon zaɓen gwamnan Kano kafin Sallar Isha’i- Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano

158
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Mohammed Wakili

Labarin da BBC ta wallafa na cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Wakili, ya ce a sanar da sakamakon zaben jihar Kano kafin Sallar Isha’i.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun kwan gaba kwan baya dangane da bayyana sakamakon zaben jihar.

Tun jiya dai ake sa ran samun sakamako zaben gwamnan jihar Kano, amma hakan bai samu ba sakamakon yunkurin kawo rikici a wurin tattara sakamakon zaben da Mataimakin Gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Murtala Sule Garo suka yi.

An shafe yinin yau ana tsammanin samun sakamako, amma har yanzu ba a bayyana ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan