Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC a jihar Kaduna ta bayyana gwamna mai ci, Nasir El-Rufa’i na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.
El-Rufa’i ya kada babban abokin hamayyarsa da tazarar kuri’a 231,259.
Jam’iyyu 38 ne suka yi takarar gwamna a jihar ta Kaduna.
Bayan aikin tattara sakamakon zaben da aka yi tsawon kwanaki biyu ana yi, Babban Jami’in Tattara Sakamakon Zaben Jihar, Farfesa Muhammad Bello ya bayyana El-Rufa’i a matsayin wanda ya lashe zaben.
Mista Bello ya ce El-Rufa’i ya samu kuri’a 1,045,427 inda ya doke abokin karawarsa na jam’iyyar PDP, Isa Ashiru wanda ya samu kuri’a 814,168.
“Cewa Nasir El-Rufa’i na jam’iyyar APC, sakamakon cika ka’idojin da doka ta tanada, kuma sakamakon samun kuri’u mafiya rinjaye an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, kuma an tabbatar da zaben sa”, in ji Farfesa Bello.
A cikin kananan hukumomi 23 da ake da su a jihar, El-Rufa’i ya lashe kananan hukumomi 14, inda abokin karawarsa na jam’iyyar PDP ya lashe kananan hukumomi tara.
Tuni jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi barazanar yin watsi da sakamakon zaben, matukar ya saba da abinda mutane suka so.
A wani taron manema labarai da ta kira ranar Litinin, jam’iyyar ta bakin Shugabanta na Jihar, Felix Hyet ta yi zargin cewa zaben cike yake da rashin bin ka’idoji da kuma magudi.