Ko Menene Dalilin Da Yasa Buhari, da Jam’iyyar APC Suka Yi Tsit Akan Rikicin Kano?

274

A yayin da ake ta cece kuce a tsakanin manyan jam’iyyun na APC mai mulkin jihar Kano da babban jam’iyyar adawa ta PDP sakamakon dakatar da tattara alkalman zaben gwamnan jihar ta Kano biyo bayan wata hatsaniya da ta afku a daren jiya a karamar hukumar Nasarawa.

Sai gashi har zuwa yanzu, uwar jam’iyyar APC ta kasa ba tace komai ba akan lamarin duk da cewa an san shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole mutum ne da baya barin sai ta kwana akan duk wani lamari da ya shafi jam’iyyar ta su.

A bangaren gwamnatin shugaba Buhari, sun yi shiru akan lamarin duk da cewa a zahiri an ga rashin gaskiya da kokarin yin magudin zabe a lamarin duk da yamadidi da kwakwazon da zaben na gwamnan jihar kano yake sha a bakunan miliyoyin yan Najeriya.

Ganin haka yasa mutane ke mamakin ko menene dalilin da yasa aka ji shiru ganin cewa jam’iyyar APC ke rike da mulki a jihar ta kano.

A daren jiya lahadi ne aka samu hatsaniya a sakatariyan INEC a karamar hukumar Nasarawa a lokacin da ake tattara kuri’u kuma a lokacin itace karamar hukumar da ta rage kafin a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan. A lokacin baturen zabe ya sanar da sakamakon kananan hukumomi 43 daga cikin 44 na jihar.

Mutanen da suka tayar da hatsaniyar sune mataimakin gwamnan jihar Nasiru Yusuf Gawuna, da kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sulen Garo da chairman na karamar hukumar inda rahotanni suka bayyana cewa sun yaga sakamakon zabe da tada hatsaniya.

Yanzu haka Humukar INEC ta shirya tsaf domin cigaba da kammala sakamakon zaben gwamnan jihar Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan