Yankin Arewa Na Da Buƙatar Jagororin Irin Sanata Kwankwaso – In Ji Sheikh Ibrahim Khalil

613

Arewa ta na da bukatar jagorori irinsu Sanatan Kano ta tsakiya, Engr Rabi’u Kwankwaso duba da irin yadda Arewa ta tsinci kanta a yanayi na rashin jagora mai kishin al’umma da kuma fada a ji a wannan yankin na arewa.

“Babbar matsalar da yankin (Arewa) ke fama da shi a ƙasar nan a halin yanzu shi ne rashin jagora guda ɗaya wanda zai jagoranci al’umma zuwa ga tudun mun tsira.”

Ya ƙara da cewa, duk wanda aka kawo akace a saka shi a gaba a matsayin shi ne jagoran yankin wanda za’a rika girmama umarninsa, sai ka ga an rufar ma sa da sara da suka na ɓatanci.

Ibrahim Khalil ya ce hatta wanda ya kawo sunan jagoran shi ma ba zai tsira daga sharrin magauta ba, sabanin yankin Yarabawa da ke kudu maso Yamma, wadanda a koda yaushe su ke yin biyayya ga jagoransu a kan alƙibla guda ɗaya tun daga kan Awolowo har zuwa yau.

A ƙarshe ya ƙara nanata wannan magana ta sa ta arewa na da bukatar mutum irinsu Kwankwaso jajurtattu, masu gaskiya da riƙon amana, waɗanda ba sa yaudara kuma su ke da cikakkun tsarin da zai ɗore.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan