Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya mayar da martani game da bayyana zaben gwamnan jihar Kano a matsayin wanda ba a kammala ba da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta yi a jihar.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a Fadarsa ranar Talata a Kano, Sarki Sanusi II ya kira ga al’ummar jihar Kano da su yi hakuri su kuma kyale INEC ta kammala aikinta, duba da yadda INEC ta bayyana zabukan gwamnoni a wasu jihohin kasar nan a matsayin wadanda ba su kammala ba.
Ya ce Hukumar Zaben nada ikon gudanar tare da sanar da sakamakon zabuka, saboda haka ya kamata a ba ta dama ta gudanar da aikinta Kano.
“INEC ta sanar da cewa zaben da aka yi a Kano ranar Asabar bai kammala ba, saboda akwai mazabu da dama da za a kara gudanar da zabe, kuma sai bayan kammala zabe a yankunan da abin ya shafa ne Hukumar za ta sanar da wanda ya yi nasara na karshe.
“Muna tunatar da jama’a cewa tuni INEC ta bayyana yawan kuri’un da dan takarar kowace jam’iyya ya samu. Wadancan kuri’u suna nan yadda suke, kuma ba wanda aka hana kuri’unsa.
“A zaben zagaye na biyu da za a yi nan gaba, kowane dan takara zai samu kuri’n da aka ba shi, kari da abinda dama tuni ya samu. Saboda haka, ya kamata mu bada hadin kai ga dukkanin hukumomin tsaro don zaman lafiya ya ci gaba da dorewa a Kano”, in ji Sarki Sanusi II.