Zazzafan Martanin Rundunar Sojojin Najriya Ga Kasar Ingila Akan Zabe 2019

137
Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Janar Yusuf Tukur Burutai da sauran jami'an soji

Rundunar Sojoji ta kasa ta mayar wa Kasar Ingila martani bisa zargin su da ta ke yi da shiga lamurran zabe dumu dumu a jihar Rivers.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ga manema labarai mai taken; Martani, kasar Ingila ta bayyana damuwarta akan yadda rundunar sojoji ta kasa ta shiga cikin zaben jihar Rivers.

Rundunar ta yi jan kunne ga kasashen duniya da su guje yin katsalandan akan al’aummaran cikin gida na kasar nan, musamman kasar Ingila, da ke zargin Sojojin da ruwa da tsaki a zaben gwamnoni, wanda hakan ba gaskiya bane.
Mai magana da yawun rundunar, col. Sagir Musa ya ce, kafin a zarge su da wani abu, ya kamata a tabbatar da zargin ta hanyar da ya dace.

Ya kara da cewa, maganar da kasar Ingila tayi ba gaskiya ba ne idan aka yi la’akari da cewa babu wani cikakken shaida da zai nuna rundunar ta shiga zaben da aka gudanar a shekarar nan kafin a fara, ko ana cikin yi ko kuma da aka gama.

Don haka, rundunar ta bayyana cewa zargin da ake musu bai da tushe, kuma ba gaskiya bane wanda hakan zai iya sauya tunanin wasu daga cikin al’umma.

Rundunar ta ce, ta samu yabo daga kungiyoyi na kasa da wajen bisa rawar da ta taka don tabbatar da anyi zaben Kasa cikin lumana tare da gaskiya da adalci. Don haka tana nan akan bakanta na zama tsaka tsaki akan al’amuran da suka shafi siyasar kasa da kuma zabe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan