Cardinal Onaiyekan Ga Yan Siyasa: Zaku Amsa Tambaya Akan Amanar Al’umma.

162

Cardinal Onaiyekan na garin Abuja ya bayyana damuwar sa bisa yadda yan siyasa da Idonsu ya rufe, suke amfani da karfi don murde zabubukan da aka yi na gwaamnoni da yan majalisu a jihohin kasarnan.

Shugaban ya fadi haka ne a jiya, a taron Catholic Bishops Conference of Nigeria (CBCN) da aka fara a jiya a garin na Abuja. Yace yin hakan, zai haifar da magudin zabe wanda zai zama tsani ga azzaluman don samun shugabanci.

Daga nan yayi kira ga shugaban kasa Buhari da ya saurari koke- koke al’umma kuma ya dauki kwakkaran matakin da ya dace.

Cardinal Onaiyekan yace zabe wata dama ce da mutane ke bi na zaben wanda zasu jagorance su, amma wasu sun mayar da shi yakin kwatar mulki ta karfin tsiya don samun karfin iko. Shi yasa zabuka suka zama yaķin a mutu ko ayi rai. Hakan yasa ake amfani da yan daba, da Jami’an tsaro, don ayi maguďin zabe ko ta halin kaka.

Daga karshe yayi kira ga yan siyasa da suji tsoron Allah sannan, da wanda ya samu mulki, da wanda ya fadi, su tuna cewa Allah ne mai bayarwa kuma Zai tambaye ka amanar Al’umma. Don haka cin zabe ta hanyar murdiya ba nasara ba ce. Tauye hakki ne na al’umma da suka fito suka yi zabe da na wanda yaci aka hana shi. Sai yayi kira ga yan siyasa da su tuba kuma su gyara don cigaban kasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan