Gaskiyar lamari game da canza Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano

54
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Mohammed Wakili

Wasu majiyoyi a Hedkwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa sun karyata jita-jitar da ake yadawa cewa an canza Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Mohammed Wakili.

Majiyoyin sun shaida wa Daily Nigerian cewa duk da matsin lamba daga Gwamnan Jihar Kano na a canza Kwamishinan ‘Yan Sandan, Rundunar ‘Yan Sanda ba ta samu wani dalili gamsasshe da zai sa a dauke shi daga jihar Kano ba.

Wani babban jami’in tsaro ya shaida wa Daily Nigerian cewa Mista Wakili wanda ya shafe shekaru 32 yana aiki da Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa zai ajiye aiki ne bisa dalilin cikar shekaru ranar 15 ga watan Mayu, 2019 lokacin da zai cika shekara 60.

“Zai ci gaba da zama a Kano har lokacin da zai yi ritaya, saboda haka babu dalilin canza shi”, in ji majiyar.

Dalilin da yasa suke so a cire shi

Biyo bayan zaben gwamnan jihar Kano
da ya nuna ba wanda ya yi nasara, Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya garzaya zuwa Abuja don kitsa kutungwilar da za ta sa a cire Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mohammed Wakil.

Jaridar Daily Nigerian ta lura da cewa jami’an ‘yan sanda a jihar sun kasance ‘yan ba ruwan mu kafin, lokacin da kuma bayan zaben, abinda ya ba dan takarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf damar samun kuri’a 1,014,747 yayinda gwamna mai ci, dan takarar jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’a 987,819.

Sahihan majiyoyi sun shaida wa Daily Nigerian cewa a cikin tawagar Ganduje da ta raka shi zuwa Abuja akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Kabiru Rurum; Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Abdullahi Abbas da babban na hannun daman gwamnan mai ba shi dabarun siyasa, Nasiru Aliko Koki.

A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, wadanda Gwamanan ke shirin kamun kafa da su a wannan bukata tasa sun hada da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshimohole; Jagoran APC na Kasa, Bola Tinubu da kuma wasu masu fada a ji dake Fadar Shugaban Kasa.

Za dai a iya tunawa cewa an samu Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinan Kananan Hukumomin, Murtala Sule Garo da Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa, Lamin Sani da hannu wajen kwace sakamakon zabe a Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe ta INEC dake Airport Road ranar Lahadi da misalin karfe 3 na dare.

An samu rahoton cewa wakilan jam’iyyu sun doki wadannan mutane guda uku, daga bisani jami’an ‘yan sanda suka tseratar da Mataimakin Gwamnan, suka kuma cafke Kwamishinan da Shugaban Karamar Hukumar.

Don kawar da halin dar-dar da ake ciki a jihar, Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya kira taron manema labarai ranar Talata a birnin Kano, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su zauna lafiya, su kuma kyale INEC ta kammala aikinta, ya kuma yaba wa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mohammed Wakili bisa yadda yake kiyaye doka da oda a jihar.

Mista Wakili, dan sanda mara tsoro dake yaki da shan muggan kwayoyi da dabar siyasa a jihar a iya cewa shi ne Kwamishinan ‘Yan Sanda wanda al’ummar jihar suka fi so a duk cikin Kwamishinonin ‘Yan Sanda da aka taba tura wa jihar.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. A gaskiya shugaban BUHARI ya kawo mana dauki a kano domin muna cikin tsaka maiwuya idan har aka sake zabe a kano zaa rasa rayuka babu adadi da dukiyoyi masu yawa, mun shiga tsaka mai wuya awannan kwannatin shiyasa Allah ya fara nuns masu ishara

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan