Zaɓukan da ba a kammala ba: INEC ta sa ranar da za a gudanar da zaɓe zagaye na biyu

40
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu a lokacin wani taron manema labarai ranar 7 ga watan Maris a Abuja

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta sa ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zabe zagaye na biyu a jihohi shida da Hukumar ta ce ba a kammala zabuka ba.

Kwamishinan INEC na Kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Ilimantar da Masu Zabe, Festus Okoye ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce za a sake gudanar da zabukan ne a jihohin Adamawa, Benue, Kano, Plateau, Sokoto da Bauchi.

Tuni INEC ta bayyana wadanda suka lashe zaben gwamna a jihohin Imo, Ogun, Kaduna, Jigawa, Lagos da sauransu.

A cewar sanarwar, sake zabukan karo na biyun ya zama dole don a samu a kammala zabukan a jihohin da abin ya shafa.

Hukumar Zaben ta Kuma bayyana cewa za a sake zabuka na biyun a mazabun da aka bayyana zabukan Majalisar Dokokin Jihohi a matsayin wadanda ba su kammala ba a dukkan jihohin da abin ya shafa.

Sanarwar ta kara da cewa an bayyana zabukan ne a matsayin wadanda ba su kammala ba saboda dalilai da dama da suka hada da amfani da Card Reader a lokacin da ake tsaka da zabe da sauransu.

INEC ta ce ta yi la’akari da rahoton da Kwamishinan Zaben Jihar Bauchi ya gabatar da ya ce an tarwatsa wata cibiyar Tattara Sakamakon Zabe a daya daga cikin kananan hukumomin jihar.

Ta ci gaba da cewa an kafa wani kwamiti wanda Kwamishinan Kasa na INEC zai jagoranta don bincikar korafe-korafen da aka gabatar ya kuma tabbatar da cewa an warware su.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan