Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da wasu gwamnonin APC guda bakwai a jiya a fadar sa dake Abuja bayan dawowarsa daga garin Daura, ba da daďe wa ba, daga hotun zabe na gwamnoni da ýan majalisun jiha.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya bayyana cewa har zuwa yanzu ba’a san dalilin da ya sa gwamnonin ganawa da shugaban kasa ba. Kuma bayan kammala ganawar, gwamnonin basu ce komai ba akan taron.
Daga bisani kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ta ce, ta jiyo rahoto daga majiya mai karfi cewa a ganawar, sun fi tattaunawa akan batun zaben jihohi 29 da aka yi.
A zaben da ya gudana na gwamnoni da yan majalisu, hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta bayyana zaben wasu jihohi guda shida a matsayin ‘bai kammalu ba’.
Ana sa ran cewa nan bada jimawa ba hukumar INEC zata sake sa ranar da za’a kara gudanar da zabe a jihohin da matsalar ta shafa.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hadar da gwamnan Borno Kashim Shettima, da Fayemi Kayode na Ekiti, da Abubakar Badaru na Jigawa, da Nasir El Rufa’i na Kaduna, da Atiku Bagudu na Kebbi, da Yahaya Bello na Kogi, da Abdulaziz Yari na Zamfara.