Zaɓukan da ba su kammala ba: Sheikh Ɗahiru Bauchi ya yi gargaɗi

160
Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga Kwamishinan Hukumar Zabe da na ‘Yan Sanda da su daina soke zabuka don biyan bukatar mutum daya.

Shehin malamin yana mayar da martani ne ga zarge-zargen da ake yi cewa duk jihohin da jam’iyyar hamayya ta PDP ke da nasara a zaben gwamnoni da aka yi a karshen mako sai a bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Shehin malamin ya bayyana haka ne a wani sakon murya da aka nada ranar Litinin a Bauchi kuma ake ci gaba da da yada shi a kafofin sada zumunta na zamani a halin yanzu.

“To akwai labarai da suke zuwa daga wasu manyan mutane wanda lallai ba za su fadi magana wadda ba haka take ba, sun ce zaben da aka yi na gwamnoni ga shi an gama lafiya, amma ana so a murde a soke wadansu zabe don a gabatar da wanda yake da baya, a gabatar da shi.

“To ina gaya wa musamman Kwamishinan Police, musamman Kwamishinan Zabe, rayukan jama’a fa suna hannunku, ku kiyaye su kar ku jefa su cikin tashin hankali da zubar da jini saboda biyan bukatar mutum daya”, in ji Sheikh Dahiru Bauchi.

Sheikh Bauchi ya ci gaba da cewa:

“Amana ce Allah Ya ba ku, Ya dora ku a kan wannan ayyuka. Ku bar zabe ya tafi yadda yake, ba soke wani don wani ya samu wucewa. A dubi jinin mutane, a dubi tada hankali, in an tada hankali a wani wuri ba a san inda zai tsaya ba. Kuma in an yi haka ku ne Allah Ya dora muku wannan nauyi, ku ne za ku dauki wannan nauyi kuma.

“Kwamishinan Police da Kwamishinan Zabe, ku bar zabe ya tafi kamar yadda yake. Kar a rika soke wadansu zabe don wani wanda yake baya ya koma gaba.

“Mutum ba zai kawo tashin hankali da fitina a kasassa, wanda aka ba shi amanar rayukan mutane da jinin mutane da dukiyar mutane da mutuncin mutane da addininsu da zaman lafiyansu yana hannunku”.

“In ku ka jawo tashin hankali da rashin zaman lafiya da gangan, to in fa ya yadu duk jinin da aka zubar yana kanku. Saboda haka nake fata za ku yi amfani da kwarewarku.

“Kwamishina na Police dole kwararren mutum ake dauka wanda ya san darajar rayukan mutane, ya san darajar jinin mutane da mutuncin mutane, sannan ya kai matsayin Kwamishina oPolice. Haka kuma, Kwamishinan Zabe, mutum ne wanda yake ya kware yana da hankali, yana da sanin darajar jinin dan Adam da dukiyar dan Adam da mutuncin dan Adam.

“Don Allah ina rokon ku, ku bar zaben nan ya tafi kamar yadda yake tafiya. Kar a soke wannan a soke wancan don wani na baya ya koma gaba. Mutum ba zai halakar da rayukan jama’a don biyan bukatar rai daya ba.

“Muna fata, abinda duk a ka shirya irin wannan don Allah don Annabi a kwantar da shi a bar zaben ya kare kamar yadda ya soma lafiya ya kare lafiya”, a kalaman Shehi.

Jihar Bauchi dai na daga cikin jihohin da INEC ta bayyana cewa zabukansu ba su kammala ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan