Fashin Baƙi: Tarnaƙin da ya hana Dimukuraɗiyya aiki a Najeriya

227

Nigeriya kasace da ta sami yancin kanta a shekarar 1960. Kuma tana daya daga cikin manya kasashe masu tasowa da karfin arzikin man fetur. a lokacin da aka sami wannan yanci da ake magana, ana lisafa Nigeriya a kasashe hudu a duniya da ake rainan dimukaradiya, wannan dalili yasa Nigeriya take rainan kanta ta fanni yanci, sai dai ansami koma baya a shekarar 1966 da aka sami juyin mulki inda akayiwa shugabannin wancan lokacin kisan gila, shekara daya da faruwar haka wani sashi na Nigeriya ya fada cikin yakin basasa a shekarar 1967. Nan fa aka sha fama har zuwa shekarar 1970 daga lokacin Nigeriya ta fara farfadowa.

Duk wanda yake biye daki-daki da tarihin dimukaradiyyar Nigeriya yana sane sarai da yadda ake shan fama daga nan zuwa nan, ba zamu kira kalubalen koma bayan dimukaradiyya a Nigeriya da wani bakon abu ba, ko koma bayanta.

Masana da yawa a kimiyar siyasa (Political Science), sun bawa dimukaradiyya, ma’ana daban-daban, wada zamu buga misali da ita awannan rubutun shine, dimukaradiyya (Democracy), wata hanyace ta bawa al’umma dama su zabi gwamnati da suke so a ransu, amma haka baya samuwa sai an sami wasu abubuwa wanda suke zaman kansu na daya akwai hukumar zabe mai zaman kanta na biyu akwai jam’iyyun siyasa, ita hukumar zabe itace hukuma mai zaman kanta, wadda bata bukatar katsalandan ko shiga cikin aikinta, haka yasa ake shirya zaben shugaban kasa, yan majalisar dattawa, wakilai da na gwamna da kuma yan majalisun jiha, duk bayan shekara hudu domin girmama tsarin dimukaradiyya.

A kowacce kasa a duniya indai ba tsarin mulkin gargajiya suke ba to lalle kuwa ana shirya zabe kuma ana nasara ana samun akasin haka ga masu neman mulki, misali a Nigeriya a shekarar 2015. Manyan yan takara guda biyu sun shiga zabe Goodluck Jonathan, shugaba mai cikakken iko na wancen lokacin da kuma Muhammad Buhari, na jam’yar adawa. Haka aka gudanar da zaben a shekarar 2015. Aka kada shugaba mai cikaken iko kuma yayi na’am da faduwa zaben da yayi, shine shugaba na farko a duniya da ya kira abokin takarar shi yayi masa murna, wannan abun ya karawa dimukaradiiyar Nigeriya kima a idon duniya.

Wanne dalili ne yasa wasu masu rike da madafun iko basa yadda da kaddarar faduwa zabe, wannan yasa zamu zamuyi nutso a ilimin sanin dan adam da zamantakewarsa (Sociology), ilimin Sociology ilimi ne wanda yashiga lungu da sako na rayiwar dan adam.

Zan dora nazari akan na Robort K. Merton, dan asalin kasar Amurka ya fara gudanar da nazarinshi na Social Structure and Anomie Abun da. Wannan nazari ke nufi shi ne a kowacce al’umma wacce ke tafiya bisa tsarin jari hujja (CAPITALISIM) mutane na rige rige samun abubuwa biyu ne. Hankoran kowa shi ne ya samu mulki, da wannan ne kuma zai yi anfani wurin samun dukiya.Kamar yadda ya ke kusan mafi yawancin kasashen duniya a yanzu su na tafiya ne a kan tsarin jari jujja Capitalism, Nigeriyarmu a yau ma tana kan wannan tsarin ne.Don haka zamu gabato da nazarin R K. Merton ga yanayin da mu ke ciki a Nigeriya, da kuma yadda ya kasafta mutane gida gida.A fili ya ke cewa yanzu a Nigeriya mu na da mabmbantan, ra’ayi akwai wanda sun tafi akan dole sai su in basuba kuma sai dai ayi ta ware, akwai kuma wanda suke da saukakan ra’ayi wanda su al’umma ne a gabansu.

Zanci gaba da wannan nazarin.

Daga
Shuaibu Lawan
shuaibu37@gmail.com
08037340560 (Sako Kawai)

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan