Hukumar Lafiya ta Duniya: Matasa Biliyan 1.1 zasu Kurmance

96

Hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO ta ce akwai yiwuwar matasa mutum biliyan 1.1 zasu kamu da matsalar kurumta a duniya. WHO ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke kaddamar da hanyoyin kare Ji na al’umma mai suna Safe Listening Toolkits to Protect Peoples Hearing, a ranar bikin Ji na Duniya (World Listening Day) a kasar Mauritius.

WHO ta ce ana bikin wannan rana domin a magance matsalar da ta shafi kurmancewa. Daga nan, hukumar tayi jan kunne ga al’umma musamman matasa masu sauraron sautin waka mai kara ko kuma na tsawon, lokaci don hakan na jawo Kurumta na har Abada.

Shugaban Hukumar, Dr Tedros Ghebreyesus yace a duk lokacin da mutum ya kurmance saboda yawan sauraron sauti mai kara, to fa ya kurmance kenan har abada wanda hakan zai kawo tsaiko ga rayuwar mutum na yau da kullum. A dalilin haka ne, hukumar ta fitar da wani ka’ida ta duniya, ta kasa da kasa mai suna International Standard On Safe Listening Devices and System, da kasashen duniya, da kamfanunnu ka, da kungiyoyin sa kai zasu yi amfani da shi don kare jin al’umma.

A nata bangaren, shugabar sashen Kurmancewa ta hukumar, Dr Shelly Chanda ta ce sun kirkiri matakai don kare Jin al’umma kuma nan gaba suna fata zasu zama a cikin kowanni wata , sannan kasashen duniya zasu yi amfani da matakan, su yi dokoki da zai kare Jin al’ummarsu.

Da ta ke karin bayani, Dr Shelly ta ce matakai na farko shi ne kirkirar wata na’ura da zai dinga fadin yawan sautin da aka saurara da tsawon lokacin da aka dauka na sauraren sautin. Sai na’urar ta rage sauti idan ya wuce kima watau Automatic Volume Reduction. Sai bama iyaye damar Iko watau Parental Control. Hakan zai ba mutane ganin irin illar da yawan sauraron sauti mai kara na tsawon lokaci, ke yi ga lafiyar Jin Dan Adam.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan