Jami’an Yansanda A Jihar Kano Sun Kama Masu Sayen Kuri’u

29

Rundunar Yansanda ta jihar Kano ta tabbatar da kama wasu mata guda biyu da maza uku a lokacin da suke kokarin sayen kuri’u a unguwanni a cikin jihar Kano.

Mai magana da yawun Rundunar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka, a jiya laraba inda yace da misalin karfe takwas na dare suka sami labarin wasu mutane da ake zargi da sayen katin daga hannun al’umma.

Mutanen sun hadar da Sa’adatu Isma’il mai shekaru 39 daga Brigade, da Haj. Halima Abba mai shekaru 55 daga unguwar Tal’udu. An kama su da katin zabe guda takwas da kudi naira 10,000. Ana zargin suna sayen katin daga naira 500 zuwa sama a hannun matan aure a unguwar Gama dake karamar hukumar Nasarawa.

Sai kuma Mukhtar Sulaiman da Idris Dan Kanawa da aka samu suna yawo a unguwar ta Gama suna neman masu sayar da katin zaben. Unguwar Gama na daya daga cikin wuraren da aka samu hatsaniya a lokacin zabe, wanda hakan yasa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta tace zaben jahar Kano bai kammala ba.

Jami’an Yansanda sun kama wani Mukhtar Shu’aibu da zargin sayen katin zabe guda biyu akan kudi naira 3,000 a unguwar Dandinshe Gabas dake karamar Hukumar Dala.
DSP Abdullahi Haruna ya kara da cewa, rundunar zata gudanar da bincike kuma zata hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki.

Daga nan DSP Abdullahi yayi kira ga al’umma da su gaggauta kaiwa rundunar rahoton duk wanda aka samu yana saye ko sayar da katin zabe, don hakan ya sabawa dokan kasa.

A karshe, yayi kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jitan da ke yawo a kafafen sadarwa akan batun cire kwamishinan Yansandar jihar Kano, Muhammad Wakili daga mukaminsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan