Zaɓen gwamnan Kano da ba a kammala ba: Abdullahi Abbas ya yi zafafan kalamai

35
Abdullahi Abbas, Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Kano

Jaridar Premium Times ta wallafa wani labari dake cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana a wani faifan bidiyo, inda aka gan shi yana siffanta zaben gwamnan Kano karo na biyu da za a yi a matsayin abin ‘a mutu ko a yi rai’.

A takaitataccen faifan bidiyon, Shugaban Jam’iyyar ya tabbatar wa da magoya baya cewa jam’iyyar APC za ta bada isasshiyar kariya ga mambobinta ko da hakan na nufin korar jami’an ‘yan sanda dake kokarin kiyaye doka da oda.

Wanda yake sanye da farar riga da farar hula, Mista Abbas yana zaune a kan kujerar roba a cikin wani gida da ake zaton nasa ne. A kewaye da shi, akwai matasa dake yi masa tafi bisa kalaman da yake yi.

Wanda ke jawabi da harshen Hausa, Mista Abbas ya ce dole masu sauraron sa da su kalubalanci duk wani yanayi da ya same su.

“Akwai yiwuwar cewa za a kama ku. Amma, bari in fada muku, kafin ku je ofishin ‘yan sanda za mu tabbatar da cewa an sake ku, kuma dan sandan da ya kama ku zai iya rasa aikinsa.

“Za mu ba ku dukkan kariyar da kuke bukata. Wannan zaben abu ne na a mutu ko a yi rai a gare mu. Dole mu ci zaben nan”, in ji Mista Abbas.

Ba jaridar Premium in ce ta nadi faifan bidiyon ba, amma bincike ya nuna cewa an dora shi a Intanet ne ranar 13 ga watan Maris.

Jihar Kano na daga cikin jihohin da aka bayyana zabukan gwamnoninsu a matsayin wadanda ba su kammala ba. Sauran jihohin su ne Plateau, Adamawa, Sokoto, Bauchi da Benue.

Kafin sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammala ba, jam’iyyar PDP na gaba da jam’iyyar APC a zaben.

Jami’an ‘yan sanda sun kama Mataimakin Gwamnan jihar, Nasir Gawuna da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Murtala Sule Garo sakamakon yunkurin kawo rikici a wajen tattara sakamakon zaben.

An kama wasu jami’ai biyu bayan nan bayan karfe biyun dare da ‘yan mintuna na daren ranar Lahadi bayan da suka isa wurin suka kuma fara tayar da hargitsi.

Wannan abu nasu ya haifar da tsaiko a sanar da sakamakon zaben a cibiyar, bayan da wasu matasa da ake zaton ‘yan daban PDP ne suka yi yunkurin kai musu hari.

Bayan nan jami’an ‘yan sanda sun saki Mista Gawuna ba tare da tuhumar sa da laifin komai ba saboda yana da kariya da Kundin Tsarin Mulki ya ba shi a matsayinsa na Mataimakin Gwamna.

Daga bisani Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ya ce ba wai kama Mataimakin Gwamnan suka yi ba, sun tseratar da shi ne daga ‘yan daban.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan