Zazzabin Doki Ya Bulla A Jihar Kaduna

277

Cutar zazzabi da ke kama dawaki ya bulla a jihar Kaduna. Cutan wanda likitoci ke kira da Equine Influenza, an ga alamun sa a jikin dawakai a wasu kananan hukumonin a jihar.

Likitocin dabbobi a jihar ta Kaduna sunce, an samu alamun wannan cuta a jikin wasu dawakai guda 18 a garin zariya da igabi wanda hakan yasa aka kebe su don gujewa yaduwar cutar.

Likitocin sun kara da cewa za’a iya gane cutan ta hanyar ganin wasu alamu a jikin dawakan da suka hadar da zazzabi, da rashin iya cin abinci, da ciwon gabbai, da zuban majina, da tari, da dai sauransu.

Kwamishinan aikin gona da dabbobi, Manzo Daniel yace gwamnati zata gaggauta hana yaduwar wannan cuta, kuma sun tanadi magunguna da allurai na riga-kafin na dawakai da sauran dabbobi. Haka zalika, za’a fara amfani da su a kananan hukumomin Kagarko, da Kajuru,da Chikun, da Giwa, da Lere. A karshe yayi kira ga masu kiwon dabbobin da su bada hadin kai ga gwamnati da likitocin don kawar da cutar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan