An gano gawar Ƙwaran da aka sace a Kano

174
Taswirar Jihar Kano

An samu gawar Injiniyan nan Kwaran da aka sace ranar Talata a Kano.

Injiniyan Kwara, ma’aikacin Kamfanin Gine-gine ne na Triacta Construction Company, yana aiki ne a Shatale-talen Dangi kafin ‘yan bindigar su sace shi ranar Talata da misalin karfe 7 na safe.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da cewa an gano gawar Kwaran ne dan kasar Lebanon a kan Titin Maiduguri ranar Alhamis da yamma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan