Home / Addini / An sace shahararren mahaddacin Kur’ani na Kano

An sace shahararren mahaddacin Kur’ani na Kano

An sace shahararren mahaddacin Kur’anin nan na jihar Kano, Sheikh Ahmad Sulaiman a kan hanyar Sheme zuwa Kankara dake jihar Katsina.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Ustaz Mujtaba Abubakar ne ya bayyana haka jim kadan bayan idar da Sallar Juma’a yau a Masallacin Juma’a na Gidan Gwamnatin Kanon.

Ya ce an sace malamin ne tare da wasu malamai biyar wadanda suke hanyarsu ta dawowa Kano daga jihar Kebbi.

“Ina kira ga wadanda suka sace wadannan malamai da su ji tsoron Allah, su tseratar da rayukan wadannan mutane da ba su ji ba ba su gani ba. Ga sauran al’ummar Musulmi, ina rokon ku yi wa wadannan malamai addu’a da kuma sauran wadanda aka sace”, in ji Babban Limamin.

Babban Limamin ya yi kira ga jami’an tsaro da su rubanya kokari don tseratar da su a raye.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta inganta tsaro a yankunan da masu sace mutane suka addaba.

About Hassan Hamza

Check Also

Yadda aka yi addu’ar cikar Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa shekara 1 a kan mulki

Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, ya jagoranci addu’a ta musamman domin murnar cikarsa shekara …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *