Sabon Matakin da Buhari ya Ɗauka na Kawo Ƙarshen HIV

173

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya ce an gudanar da binciken Safiyon NAIIS, watau Nigeria HIV/AIDS Indicator and Impact Survey domin samun ingantattun alkalumma da kasa take bukata wajen kawo karshen cutar mai karya garkuwar jiki.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya alhamis, a fadarsa dake garin Abuja, yayin da yake kaddamar da rahoton safiyon NAIIS.

Shugaban ya kara da cewa a cikin rahoton aka samu, akwai kiyasin cewa a kalla yan Najeriya miliyan daya da dubu dari tara da ke rayuwa da cutar kanjamau kuma akalla muyum miliyan daya ke karbar magani.

Baya ga haka, shugaba Buhari ya nuna jin dadin sa na ganin kyakkyawar makoma da kasarnan ta ke da shi na kawo karshen cutar Kanjamau da ya kashe mata da maza da dama. Yace hakan zai bada damar kawo karshen cutar zuwa shekarar 2030 ta hanyar aiki tukuru don cimma wannan muradin.

Ministan lafiya, mista Isaac Adewole yace yanzu Najeriya ta sakko zuwa matsayi na hudu a duniya a cikin kasashen da ke da mutane masu dauke da cutar kanjamau inda kasashen South Afrika da India, da Mozambique ke gaba da ita a madadin da matsayi na biyu da ta ke a da.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan