Home / Labarai / Ko Kunsan Sabon Zargin da PDP Ta Yiwa Buhari da APC?

Ko Kunsan Sabon Zargin da PDP Ta Yiwa Buhari da APC?

Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC da shirin yin amfani da sojoji da sauran jami’an tsaro wurin tsorata mutane a zaben da za’a sake a jihar Sokoto.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Sokoto Alh Ibrahim Milgoma ne ya bayyana haka jiya alhamis inda ya ce suna da tabbacin gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne zai cinye zaben da za’a sake ranar 23 ga watan nan.

Jam’iyyar PDP ta gargadi jam’iyar APC da ta bar tunani yin mafani da jami’an tsaro don tursasa wa jama’ar jihar wanda basa so.

Ya kara da cewa jihar Sokoto jihar ce da jama’ar ta ke son zaman lafiya kuma masu bin doka don haka bai dace hana su abinda suka zaba ba.

Daga nan yayi kira ga gwamnati da ta bar jama’a su zabi wanda suke so a zaben da za’a sake a jihar.

A karshe yace jihar Sokoto, tana daukan matsayin Umma ga makotan jihohi don haka yana da kyau su girmama ta ba wai a hada kai da su a mayar da jihar dandali na yakin cin zabe, da za’a daura wa mutane

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Rugujewar Kwankwasiyya ta kunno kai a jihar Kano – Fa’izu Alfindiki

Fitaccen mai adawa da tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *