Home / Gwamnati / An sako surukar Masari

An sako surukar Masari

A ranar Juma’a ne Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa wadanda suka yi garkuwa da surukar Gwamna Masari, Hajiya Hauwa Yusuf sun sake ta.

Ranar Alhamis ne aka saki dattijuwar ‘yar shekara 80.
Amma dai ba a sani ba ko an biya kudin fansa ba kafin sakin nata.
Kakakin Rundunar, SP Gambo Isah wanda ya tabbatar da sakinta ya fada a wata sanarwa cewa:”Ina mai farin cikin tabbatar muku da cewa wadanda suka yi garkuwa da surukar Mai Girma Gwamna, Aminu Bello Masari ranar Alhamis, 14 ga watan Maris da misalin karfe 4 na yamma sun sake ta.

“Lafiyar ta kalau. Tuni an hada ta da iyalinta bayan an yi mata gwaje-gwajen lafiya da suka wajaba”, in ji Kakakin.

Mai shekaru 80, Hajiya Hauwa ita ce mahaifiyar Binta Yusuf, daya daga cikin mata uku na Gwamana Masari.
Za dai a iya tuna cewa ranar Juma’a, 8 ga watan Maris ne masu garkuwa da mutane ne suka sace surukar Gwamnan.

About Hassan Hamza

Check Also

Ba Za Mu Yadda Da Duk Wani Yunƙurin Juyin Mulki Ba— Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗi ga masu kira a gare ta domin ta ƙwaci …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *