Jam’iyyar PDP: Muna da Tabbacin Lashe Zaben Gwamnoni.

43
Sakataren Yaďa Labaran Jam’iyyar PDP mista Kola Ologbodiya

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa zata lashe zabukan gwamna da za a sake a kasarnan. Jam’iyyar ta fadi hakan ne ta bakin sakataren yada labaran ta misat Kola Ologbodiya a jiya lahadi, 17 ga watan maris.

Mista Ologbodiya ya kara da cewa suna da tabbacin samu nasara a zabukan da za a gudanar don haka jam’iyya mai mulki zata sha kaye.

Jam’iyyar ta PDP ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da kokarin murde zabukan da aka yi ta hanyar amfani da jami’an tsaro, tare da yunkurin kawo hatsaniya a lokacin da ake zabuka don samun damar magudi.

Jam’iyyar ta kara da cewa, duk da haka sai gashi jam’iyyar APC na yiwa duniya kururuwa bayan ita ce ke amfani da karfin iko wajen tafka maguďin zabe.

Jam’iyyar PDP ta ce daga kuri’un da aka kirga a jihohin Adamawa, da Bauchi, da Benue, da Kano, da Plateau, da Sokoto sun nuna cewa ita ce ke kan gaba da gagarumar nasara don haka babu shakka su zasu lashe zaben da za a maimaita.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan