Home / Siyasa / Sake zabe a wasu wurare a Kano: Bashir Tofa ya ja hankali
Alhaji Bashir Othman Tofa

Sake zabe a wasu wurare a Kano: Bashir Tofa ya ja hankali

Shahararren dan siyasar nan na Najeriya, Alhaji Bashir Othman Tofa ya yi kira ga manyan ‘yan takarar gwamnan Kano da su rungumi kaddara ga duk wanda ya fadi zabe.

Bashir Tofa ya bayyana haka ne a yayin wata hira da BBC.

Bashir Tofa wanda shi ne Shugaban Wata Kungiyar Ci Gaban Kano mai suna Kano Concerned Citizens Initiative, KCCI, ya bayyana fargabar samun tashin hankali matukar a ka yi yunkurin sauya sakamakon zabe da za a yi a wasu yankuna a Kano.

“Yanzu hakkin INEC ne ta fitar da abin da yake shi ne halal wanda za a yadda da shi ko da an tafi kotu,”, a hirarsa da BBC.
Ya kuma yi kira ga ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar da su ja hankalin magoya bayansu su zauna lafiya.

A ranar Asabar 23 ga watan Maris ne INEC ta ce za ta sake zaben gwamna a wasu yankunan Kano bayan da ta sanar da cewa ba a kammala zaben jihar ba da aka yi ranar 9 ga watan Maris.

A cewar BBC, fafatawar a zaben da za a sake a Kano ta shafi ‘yan takarar manyan jam’iyyu biyu ne; gwamna Ganduje na APC da kuma babban mai hamayya da shi Abba Kabir Yusuf na PDP.

Alhaji Bashir Tofa ya taba yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar NRC a 1993 a zamanin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

About Hassan Hamza

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *