Waɗanda suka garkuwa da Sheikh Ahmad Sulaiman na buƙatar maƙudan kuɗaɗe kafin su sake shi

144
Sheikh Ahmad Sulaiman

Wadanda suka yi garkuwa da Sheikh Ahmad Sulaiman, shahararren malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano sun bukaci a biya Miliyan 300 a matsayin kudin fansar da za su sake shi da sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su tare da shi.

An sace Sheikh Ahmad ne ranar Alhamis a kan hanyar Sheme zuwa Kankara yayinda suke dawowa daga jihar Kebbi.

A wata hira ta musamman da jaridar The Guardian, wani dan gidan Malam Ahmad din, Isma’il Bunyaminu ya tabbatar da cewa wadannan suka yi garkuwa da malamin sun tuntubi iyalinsa.

“Wadannan suka yi garkuwa da shi sun tuntube mu, kuma muna tattaunawa da su”, Bunyaminu ya fada wa The Guardian haka.

Bunyaminu ya ce a halin yanzu ana kokarin hada wadannan makudan kudade, kuma tuni iyalinsa sun tuntubi Gwamnatin Jihar Kano da shugabancin Kungiyar Izala ta Kasa, JIBWIS.

Lokacin da aka tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi ya ce ba shi da masaniya game da al’amarin saboda ba huruminsa ba ne.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan