Kano Ta Zama Mizanin Auna Adalcin Hukumar INEC Inji Kwankwaso

281

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sen Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa zaben gwamna da za a kammala a jihar ta Kano zai zama ma’aunin adalcin hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC).

Sen Kwankwaso ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da yayi da BBC Hausa.

Sanatan ya kara da cewa zaben gaskiya shi zai tabbatar da darajar gwamnati da na hukumar INEC, idan sunyi adalci ko kuma ya ruguje ta idan suka yi rashin adalci.

Hakan kuwa yana alakantuwa ne bisa yadda zaben na jihar Kano ya ja hankulan al’ummar Kasarnan da ma wasu Kasashen.

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da hukumar INEC ta ce zabensu bai kammalu ba, kuma za a sake zabe a ranar 23 ga watan maris.

A zaben gwamna da ya gudana ranar 9 ga watan maris, sakamakon da aka tattara na jihar Kano ya nuna cewa jam’iyyar adawa ta PDP ce akan gana da kuri’u miliyan 1,014,343 yayin da jam’iyya mai mulkin jihar na APC nada kuri’i dubu 987,829

Daga baya hukumat INEC ta soke kuri’un wasu mazabu sakamakon laifukan tada hatsaniya, da samun arigizon kuri’u, da sayen kuri’u da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan