Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai sa baki a cikin maganar maimaita zabe da za a yi a wasu jihohin kasar nan ba. Shugaban yayi jan kunne ga magoya bayan jam’iyyarsa ta APC da su fita a cikin lamarin domin shi ba zai sa baki a cikin sakamakon zabukan ba.
Shugaban ya bayyana haka ta hannun mai bashi shawara akan harkokin yada labarai malam Garba Shehu.
Garba Shehu ya rawaito cewa shugaba Buhari ya ce hukumar INEC ita ce kadai ke da wuka da nama akan duk wani zabe da za a gudanar a kasar nan.
Don haka, shugaban yayi kira ga ýaýan jam’iyyarsa ta APC da su nemi kuri’unsu a wurin jama’a domin shi ba zai sa hannun a lamarin ba.
Sanarwan yayi duba tare da suka ga zargin da ke yawo cewa wasu ýaýan jam’iyyar APC na kokarin ganin shugaba Buhari yayi amfani da karfin iko don murde zabe, da kuma masu ganin lafin shugaban na nuna halin ko in kula akan zabukan gwamnonin jihohin kasar.
Garba Shehu ya ce kundin tsarin mulki bai ba shigan kasa ikon tsoma baki a cikin hatkar zaben kasa ba, don haka ba zai yi abinda zai karya tanade-tanaden kundin tsarin mulki kasa ba.
Bugu da kari, hukumar INEC tana cin gashin kanta ne, kuma zata cigaba da aiki ba tare da tsoma baki da shugaba Buhari ba.