Zargin wasu gwamnoni da tsoma baki a siyasar Kano- Tinubu ya mayar da martani

299

A ranar Laraba ne Jagoran Jam’iyyar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana tsoma baki a zaɓen jihar Kano da za a sake.


Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen watsa labarai, Tunda Rahman ya raba wa manema labarai a Legas ranar Laraba

Mista Tinubu ya ce hotonsa da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai ana nuna shi tare da Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano an ɗauke shi ne tun a 2018 lokacin da Gwamnan ya kai ziyara Legas.


A cewarsa, irin wannan jita-jitar tana cutar da dimokuraɗiyyar da Najeriya ke son kafawa, kuma ta saɓa da siyasar ci gaba da aka san jihar Kano da ita.


“Suna amfani da karya da yaudara a matsayin abin cimma muradinsu, suna nuna ni a matsayin wani mutum ɗaya mai tasiri a siyasa da zai iya canza alƙiblar zaɓen gwamnan.


“Don a sani, ban zo Kano ba kuma ba wani lokaci da na zo Kano a lokacin da ake gudanar da waɗannan zaɓuka.


“Hotan da waɗannan maƙaryata ke yaɗawa shi ne wanda aka ɗauka lokacin da gwamnan ya ziyarci Legas”, in ji Mista Tinubu.


Ya ce a tarihance, Kano ta kasance wata cibiyar siyasar ci gaba.


A cewar Mista Tinubu, tsarin siyasar Kano ne ta taimaka wajen kafa jam’iyyar APC.

“Kano tana da masu zaɓe wayayyu waɗanda suke zaɓe yadda suka yi amanna. Ina fata za su yi watsi da karyace-karyace da jita-jitar da ake yaɗawa game da ni, su ci gaba da riƙe siyasarsu ta ci gaba”, a kalaman Mista Tinubu.


Tinubu ya ce ya kasance a gaba-gaba wajen kawo gyare-gyaren zaɓe, yin adalci da daidaito, kuma ba zai yi wani abu da zai ɓata waɗannan kyawawan halaye ba.


Tinubu ya ce ya yadda da zaɓe na adalci, kuma shi ne ma abinda ya shafe tsawon rayuwarsa yana karewa.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan