Dandazon ‘yan Kwankwasiyya sun kai wa Kwankwaso ziyara

43


Dandazon magoya bayan jam’iyyar PDP mazauna unguwar Gama dake ƙaramar hukumar Nasarawa ne suka yi tsinke a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso don su nuna goyon bayansu gare shi bisa ziyarar da aka shirya zai kai unguwar amma daga baya ya soke bisa dalilan tsaro.


‘Yan Kwankwasiyyr dake sanye da jajayen huluna an gan su riƙe da kwalaye dake ɗauke da rubutu daban-daban kamar “Gama ta Abba ce”.

Daily Nigerian ta gano cewa soke ziyarar ya biyo bayan wani rahoton sirri da jam’iyyar PDP ta samu dake cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jibge ‘yan daba don su kai wa Kwankwaso, ɗan takarar gwamna a jam’iyya PDP da magoya bayansu hari.


An kuma gano cewa an so a tayar da rikici a yankin na Gama ne don a nuna cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Mohammed Wakili ya gaza wajen bada tsaro.


Wakilin Daily Nigerian ya gano cewa dandazon magoya bayan Kwankwasiya ne ke ta yin tsinke a gidan Kwankwaso don nuna goyon bayansu bisa zaɓen da za a sake a wasu yankunan jihar Kano.


“Mun fasa kai ziyarar da muka shirya zuwa Gama, biyo bayan samun rahoton sirri dake cewa Ganduje ya jibge ‘yan daba da za su kai wa RMK hari don a nuna hakan a matsayin gazawar Mista Wakili wajen ba Kano tsaro. Amma, mutanen Gama suna ta yin tsinke zuwa gidan RMK”, a cewar wani ɗan cikin Kwankwasiyya.


A cewar ɗaya daga cikin magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar wanda aka sani da Dadiyata a Twitter, an jiyo Kwankwasiyy yana cewa: “Birninmu na siyasa bai fi darajar ɗigo ɗaya na jinin ɗan Kano ba”.
Gama dai ita ce mazaɓa mafi girma daga cikin mazaɓun da za a sake zaɓe.
Mazaɓar dake da masu rijistar katin zaɓe fiye da 47000, an yi amannar yanki ne da jam’iyyar PDP ke da ƙarfi.


Biyo bayan bayyana zaɓen gwamnan Kano a matsayin wanda bai kammala ba, ɗan takarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf da gwamna mai ci, kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje sun ta gudanar da yaƙin neman zaɓe a yankin don jan hankalin masu zaɓe gabanin zaɓen da za a sake ranar 23 ga watan Maris.


Hakan ta sa Ganduje fara gudanar da aikace-aikace a mazaɓar da suka haɗa da gine-ginen hanyoyin, gina fanfunan burtsatse da ba mata da maza jari.

Dandazon ‘yan Kwankwasiyy a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan