Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya fara aiwatar da wasu manyan aiyyukan raya kasa a mazabar Gama.
Gwamnan yayi bayani a wata hira da yayi a shafin BBC inda ya ce aiyyukan da ake yi yanzu, tuni suna cikin wanda gwamnati ta tsara tun fil-azal. Wadannan aiyyuka dama suna kan layi, amma sai a wannan karo ne Allah ya sa zasu yi shi.
Abin lura anan shi ne mazabar Gama ce mazabar da aka samu hatsaniya a lokacin tattara kuri’u, wanda hakan yasa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar Kano a matsayin bai kammalu ba.
Yanzu haka a kwanaki kadan da suka rage kafin ranar karasa zaben gwamna a jihar ta Kano, jama’ar mazabar Gama wacce kuri’un ta zai taka muhimmiyar rawa akan sakamakon zabe.
A ýan kwanakin nan, jama’ar mazabar Gama sun wayi gari sun ga gwamnati na aiwatar da manyan aiyyukan raya kasa a yankinsu duk da cewa sun shafe shekaru da dama suna fama da kalubale na karancin ruwa, da hanyoyi, da asibitoci da sauransu ba tare da gwamnati ta agaza musu ba.
Jama’a da dama a yankin suna ganin cewa gwamnati na gudanar da aiyyukan ne don samun kuri’un su a zaben ranar Asabar. Rahotanni da aka samu sun nuna cewa jami’an Yansanda a jihar ta kama masu sayen kuri’u a mazabar ta Gama.
Mazabar ta Gama da ke karamar hukumar Nasarawa tafi daukan hankali fiye da sauran mazabu da za a sake zabe a ranar Asabar me zuwa.