Jam’iyyar APC Zata Sa Damakaraďiyya A Cikin Hatsari inji PDP

167

Jam’iyyar PDP tayi Allah Wadai da dakatarwar da kotu tayi na kammala sakamakon zaben gwamna a jihar Bauchi inda ta ce jam’iyyar APC ce ta ke kokarin amfani da bangare shari’a don kawo tsaiko ga tattara kuri’un ganin cewa ita ce ke samun nasara.

Jam’iyyar PDP ta bayyana hakan ajiya laraba 20 ga watam maris, ta hannun sakataran yada labaran ta mista Kola Olgbondiyan a shafin ta na Facebook.
PDP tayi gargaďin cewa muddin aka cigaba da sa idanu jam’iyyar APC na katsalandan a harkokin zabe, babu shakka damakaraďiyyar mu zata shiga cikin hatsari kuma zamu tsinci kanmu a yanayi na tabarbarewan doka da oda.

Mr Ologbondiyan ya ce hukumar INEC ce kadai ta ke da ikon kidaya kuri’u, ko dakatar da kidayar, ko kuma cigaba da kidaya kuri’u kamar yadda ya faru a jihar Bauchi. Sannan muddin ba a gama kidaya kuri’u an sanar da sakamakon zabe ba., babu wanda doka ta bawa ikon yin katsalandan ga hukumar INEC.

Ya kara da cewa, a sashe na takwas karkashin sashe na goma cikin baka na dokar hukumar zabe ya ce kotu bata da ikon zartar da wani hukunci ko bayar da umarni na dakatar da zaben cikin gida ko babban zabe, ko sauran harkokin zabe.

Da wannan jam’iyyar PDP tayi kira ga hukumar INEC da ta cigaba da aikinta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada. Sai kuma ta yi kira ga fannin shari’a da su guji biyewa jam’iyyar APC tana sa su aikata abinda ka iya jefa su a cikin matsala ko ma ya jawo salwantar damakaraďiyya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan