Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da jami’an tsaro da su tabbatar da cewa anyi zaben cike gurbi a jihar Kano ba tare da wata tangarďa ba.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne cikin wani sanarwa da ta fitar a jiya laraba, 20 ga watan maris ta hannun shugaban ta na rikon kwarya malam Rabi’u Sulaiman Bichi.
A cikin sanarwan, malam Rabi’u Bichi yayi kira ga hukumar INEC da jami’an tsaro da su guji daukan bangare a lokacin zaben.
Ya kara da cewa, hakkin jami’an tsaro ne su kare al’umma da kuri’unsu daga cin muttunci, da wulakanci, da magudi daga kowanni bangare.
Sannan yayi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da ya ja hankali yan siyasa da shugabannin addainai, da yan kasuwa, da masu sarautun gargajiya a fadin jihar da su kasance masu yaďa akidar zaman lafiya a lokacin zabe.
Sai ya kara da cewa shugaban kasa yayi amfani da mukaminsa don ganin anyi zabe cikin lumana kuma ya fahimtar da gwamnatin jihar Kano hakan saboda a samu kwanciyar hankali.
Daga nan yayi kira ga hukimar INEC da ta kasance mai gaskiya da adalci, kuma ta tsaya tsayin daka don gudanar da sahihin zabe, kuma duk wanda yayi kokarin kawo matsala a cikin zaben, to hukumar tayi hukunci yanda ya kamata.
Daga karshe ya bawa hukumar INEC shawarwari akan hanyoyin da zata bi don yin maganin masu kokarin yin magudin zabe a jihar domin akwai rade-radin an shirya amfani da yan daba, da wasu jami’an tsaro da masu sayen katin zabe da sauransu don tafka magudi.