INEC ta turo ƙarin Kwamishinonin Zaɓe zuwa Kano

127


Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta turo wasu ƙarin Kwamishinonin Zaɓe uku zuwa jihar Kano don gudanar da zaɓen gwamna da za a sake a wasu yankunan jihar ranar 23 ga watan Maris.


ihar Kano dai na daga cikin jihohi shida da INEC ta bayyana zaɓukan gwamnonisu a matsayin waɗanda ba su kammala ba.


A ranar Alhamis ne Kwamishinan Hukumar Zaɓen ta Jihar Kano Farfesa Riskwa Shehu ya bayyana a wani taron manema labarai cewa jihar Kano ta samu ƙarin Kwamishinonin Zaɓe uku.


Ya ce sababbin Kwamishinan Zaɓen su ne; Asma’u Maikuɗi daga jihar Zamfara; Ganiyu Rabi’u daga jihar Ogun, sai Ahmad Mahmud daga jihar Kebbi.


Farfesa Shehu ya bayyana cewa Hukumar a shirye take wajen gudanar da zaɓen na ranar Asabar, inda ya ce a yau Juma’a ne za ta fara raba kayan aikin zaɓe masu buƙatar kulawa sosai.


Farfesa Shehu ya ce za a gudanar da zaɓen ne a ƙananan hukumomi 28 da suke da wuraren yin rijista har 75 a mazaɓu 207 waɗanda aka soke zaɓukansu.


Ana sa ran mutane masu rijistar zaɓe 128,334 ne za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan da za a sake.


Farfesa Shehu ya ce an soke zaɓukan a ƙananan hukumomin ne sakamakon rikice-rikice da kuma yin zaɓe fiye da yawan masu rijista.


“An soke ƙananan hukumomi 15 da suke da mazaɓu 116 sakamakon samun rikice-rikice, yayinda aka soke ƙananan hukumomi 23 dake da mazaɓu 91 sakamakon kaɗa ƙuri’a fiye da yawan masu rijista.


“Haka kuma, mun karɓi dukkan kayayyakin aiki masu buƙatar kulawa da waɗanda ba sa buƙatar kulawa, kuma Hukumar za ta fara raba kayan aikin zuwa yankunan da abin ya shafa ranar Juma’a da safe”, in ji shi.


Farfesa Shehu ya yi kira ga kafafen watsa labarai da su bada sahihan rahotonnin zaɓen, yana mai kira a gare su da su guje wa yaɗa labaran ƙarya waɗanda ka iya jawo tada zaune tsaye a jihar.


Ya ƙara bayyana kuɗirinsa na gudanar da sahihin zaɓe, yana mai kira ga al’umma da su kasance masu kyakkyawar ɗabi’a da kiyaye doka kafin, lokacin da bayan kammala zaɓe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan